Kamfanin rarraba hasken wutar Lantarki na Kasa TCN ya bayyana cewa wasu daga cikin sassan birnin tarayya Abuja za su fuskanci katsewar wutar lantarki a karshen makonan, bisa gyaran da za ayiwa na’urorin samar da wutar.

Kamfanin ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Juma’a, inda ya ce an saba gudanar da aikin ne kowacce shekarar.
Sanarwar ta ce za a fara yin aikin ne daga yau Asabar zuwa gobe Lahadi, inda kuma za a samu katserwar wutar a yankunan da abin ya shafa na tsawon sa’o’i bakwai a kowacce rana.

TCN ya kara da cewa za a gudanar da aikin ne daga karfe 9:00 na safiya zuwa karfe 4:00 na yammaci.
