Jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano ta dakatar da sanata mai wakiltar kudancin Kano Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila, tare da wasu ƴan majalisun tarayya guda uku.

Sauran ƴan majalisun wakilan da aka dakatar sun haɗar da Ali Sani Madakin Gini mai wakiltar ƙaramar hukumar Dala, Abdullahi Sani Rogo mai wakiltar ƙananan hukumomin Rogo da Ƙaraye, sai kuma Kabiru Alasan Rurum mai wakiltar ƙananan Rano, Kibiya da Bunkure.

Shugaban jam’iyyar ta NNPP na jihar Kano Hashimu Sulaiman Dungurawa ne ya sanar da hakan, yayin wata tattaunawa da manema labarai a yau Litinin, inda ya ce an hukunta su ne bisa zargin yi wa jam’iyyar ta NNPP zagon ƙasa.

Dungurawa ya shaida cewa zaɓaɓɓun ƴan majalisar da aka zaɓe su ƙarƙashin inuwar jam’iyyar ta NNPP, sun shiga yin ayyukun da su ka saɓa da gwadaben jam’iyyar a kwana-kwanan nan.

Inda ya soke su da gaza karewa da ɗaga martabar jam’iyyar, duk kuwa da halaccin da aka yi musu na basu takara a lokacin zaɓe.

Ɗaya daga cikin babban dalilin da ya janyo dakatar da sanata Kawu Sumaila shi ne, taron aurar da ƴarsa da kuma ƙaddamar da wasu ayyuka a jami’a mallakinsa da ke garin Sumaila, inda ya gayyaci jiga-jigan ƴan jam’iyyar APC ciki har da shugaban jam’iyyar na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje.

Dungurawa ya bayyana mamakinsa ganin yadda Kawun ya gayyaci mutanen da su ka yaƙe shi a baya, yayin da kuma ya share mutanensu na jam’iyyar NNPP.

A ƙarshe ya bayyana cewa Ƙofar yin sulhu har yanzu a buɗe ta ke, idan har waɗanda aka dakatar sun yarda da kuskurensu kuma sun nemi afuwa, jam’iyyar za ta iya dawo da su.

Sai dai bayan dakatarwa da jam’iyyar ta yiwa ‘yan Majalisar, Kawu Sumaila Yayi Watsi da dakatarwar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: