Matar Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Godswill Akpabio, Ekaette Akpabio, ta yi barazanar daukar matakin shari’a da Sanata Natasha Akpoti da ta zargi mijinta da yunkurin yin lalata da ita.

Matar Akpabio ta bayyana hakan ne ta cikin wata hira da manema labarai da ta yi a jiya Juma’a.

Ekaette ta ce babu gaskiya a cikin kalaman Natasha, kuma ta yi hakan ne domin batawa mai gidan nasa suna.
Acewar Matar ta Akpabio za ta tabbatar da ganin ta kwatarwa kanta ‘yanci a Kotu bisa cin zarafin da Nashata ta yiwa mai gidanta, don kare martabar mijinta daga zargin.

Ekaette ta kara da cewa mijinta mutum ne mai daraja mata, inda ta ce tun kafin zamowarsa shugaban Majalisar dattawa ya ke kokarin ganin mata sun samu dama a cikin gwamnati.

Leave a Reply

%d bloggers like this: