Wani mummunan harin bom daga ƴan ƙunar baƙin wake ya hallaka mutane fararen hula 12 a ƙasar Pakistan, cikinsu harda ƙananan yara shida.

Lamarin dai ya auku ne a Arewa maso Yammacin ƙasar a jiya Talata, yayin da wasu mahara su biyu su ka tuƙo mota ɗauke da abin fashewar zuwa wajen jami’an tsaro da ƴan sanda.

Gagarumin harin dai ya haifar da yaɗuwar hatsaniya tare da rikito da rufin wani Masallaci da ke kusa da wajen, a daidai lokacin da mazauna yankin su ke gudanar da buɗa bakin ibadar azumin watan Ramadan.

Harin kuma dai ya shafi cunkoson hada-hadar kasuwanci a wajen, tare da jikkata wasu mutanen da kuma lalata gine-gine.

Jami’an tsaro sun samu nasarar daƙile maharan daga shiga sansanin sojojin wajen, bayan sun yi artabun musayar wuta da su tare da hallaka mutane shida daga cikinsu.

Kawo yanzu dai babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin kai harin, sai dai a ƴan kwanakin nan ƙungiyar ƴan Taliban ta Pakistan ta tsaurara tsangwama ga jami’an tsaro, musamman a yankunan da su ka yi iyaka da ƙasar Afghanistan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: