Jami’an sojin Najeriya na Operation Fansan Yamma a Jihar Zamfara sun samu nasarar hallaka wani dan ta’adda mai suna Yellow Aboki, wanda ya kasance aboki ne ga dan ta’addan nan da aka jami’an suka hallaka mai suna Hassan Bamamu.

A wata wallafa da mai sharhi kan sha’anin tsaro Zagazola Makama ya fitar a yau Litinin, ya ce jami’an sun hallaka Aboki ne a lokacin da suke gudanar da sintiri a karamar hukumar Tsafe ta Jihar.

Wasu Majiyoyin tsaro sun shaidawa Makama cewa jami’an sojin sun hallaka Yellow Aboki ne mako guda da hallaka abokin ta’addancin nasa Hassan Bamamu, wanda hakan ya sanya Yellow ya kara kai mi fiye da baya wajen aikata ta’addanci a Jihar ta Zamfara.

Yellow dai na aikata ta’addancin ne a yankunan Bamamu, Agama-Lafiya, Dan Mali, kuma Makera.

Leave a Reply

%d bloggers like this: