Jam’iyyar APC a Jihar Rivers ta bukaci da gwamnan Jihar Siminalayi Fubara karkashin jam’iyyar PDP da yayi murabus daga kujerarsa ta Gwamnan Jihar.

Jam’iyyar ta bai’wa gwamna Fubara wa’adin sa’o’i 48 da ya yi murabus din ko kuma Majalisar dokokin Jihar ta dauki matakin tsige shi daga kan kujerarsa.

Shugaban Jam’iyyar APC a Jihar Cif Tony Okocha ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai a yau Litinin a garin Fatakwal babban birnin Jihar.

Shugaban jam’iyyar na Jihar na zargin Fubara da cin zarafin shugaban Kasa Bola Tinubu, a lokacin da shugaban ke ke kokarin samarwa da Jihar Mafita akan rikicin da ke faruwa a cikinta.

Okocha ya bayyana cewa kokarin cin zarafin shugaban Kasa da Fubara yayi hakan kadai ya isa a sauke shi daga kan kujerar gwamnan.

Acewarsa Jam’iyyar APC a Jihar ba za ta tsaya ta sanya idanu ba, Fubara na raina shugaban Kasa ba, inda ya ce kotun koli ma ta tabbatar da hakan, tare da samar da wasu shaidun akansa.

Tony Okocha ya bukaci da Fubara da ya gaggauta sauka daga shugabancin Jihar cikin salama, ko kuma a dauki matakin tsige shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: