Jami’an sojin Najeriya ƙarƙashin dakarun Operation Hadin Kai sun kubutar da mutane 77 daga dajin Sambisa na jihar Borno.

Da yake mika mutanen ga gwamnatin jihar jiya Litinin, kwamandan rukuni na 7 Manjo Janar Shaibu ya ce waɗanda aka kubutar sun hada da maza bakwai, mata 34 da yara 34.

Kwamandan wanda mataimakinsa Birgediya Janar Akpodu ya wakilta, ya ce an kubutar da mutanen ne yayin dasu ka kai wani sumamen haɗin gwiwa.

Wuraren da su ka kaddamr da aikin akwai Ukuba, Sabil Huda, Garin Fajula da kuma Gobara.

A wajen harin da su ka kai sun lalata kayyakin mayan Boko Haram da kuma hallaka da yawa daga cikinsu da makamansu.

Waɗanda aka kujutar an mikasu ga mahukuntan gwamnatin jihar Borno.

Da take karbarsu a madadin gwamnan jihar, Hajiya Zuwaira Gambo kwamishinar mata a jihar ta yabawa jami’an bisa namijin kokarin da su ka yi wajen kubutar da mutanen.

Leave a Reply

%d bloggers like this: