Fadar shugaban ƙasa a Najeriya ta ce tsarin da shugaban ke kai wajen tafiyar da mulkin ƙasar ya na kan daidai.

Wannan dai martani ne da fadar ta yi ga ƙungiyar limaman kiristoci tsagen katolika.

Kungiyar limaman ta ce tun bayan hawan shugaba Bola Ahmed Tinubu miliyoyin mutane su ka fada cikin talauci saboda tsauraran manufofinsa.

Sai dai a wata sanarwa da hadimin shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar, ya ce wuraren da kungiyar ya kalubalanta kamar tsaro, tattalin arziki, da samar da aikin yi ana samun nasara matuƙa

A cewarsa, a ɓangaren tsaro fiye da ƴan ta’adda da masu garkuwa da ƴan fashi sana da 8,000 aka hallaka cikin shekaru biyu.

Haka zalika akwai mayaƙan Boko Haram sama da 10,000 da aka kashe cikin shekarun

Sannan akwai mutane dubbai da aka kubutar daga wajen masu garkuwa wanda su ka haɗa da mata da kananan yara.

Sakamakon cigaban da aka samu a bangaren, ya ce manoma a jihohin Kaduna, Kebbi, Jigawa sun koma gonakin su.

Haka a ɓangaren samar da aikin yi ya ce akwai tsaruka daban-daban fa gwamnatin tarayya ta bijiro da su don samar da aikin yi a tsakanin matasa.

Kungiyar dai ta zargi gwamnatin shugaba Tinubu da kayar da al’amuran ƙasar baya ta hanyar jefa miliyoyin mutane cikin matsancin talauci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: