Bayan hallaka shugaban ƴan Lakurawa a jihar Kebbi mayaƙan sun kai harin ramuwa inda su ka kashe mutane 13.

Mayaƙan Lakurawa sun hallaka mutanen a Birnin Dede da ke karamar hukumar Arewa a jihar ranar Lahadi.

Hakan na zuwa ne bayan hallaka shugaban kungiyar Maigemu.

Wani a garin mai suna Musa Gado ya ce yan Lakurawan sun cinna wuta a ƙauyika guda takwas bayan da su ka buɗe musu wuta

Sai dai ƙauye ɗaya ne ya tsira wanda jami’an soji ke gadinsu.

Wani mai suna Sulaiman Abubakar ya shaida cewar, mayaƙan sun shiga kauyensu da daddare bayan sallar magariba.

Ya ce harin ya rutsa da mata da kananan yara.

A cewarsa sun hallaka mutane da dama sannan su ka konesu .

Ƙauyukan da lamarin ya shafa sun hada da Birnin Garin Nagoro, Yar Goru, Dan Marke da Tambo.

Shugaban ƙaramar hukumar Arewa Sani Aliyu ta tabbatar da kai harin

Ya ce an aike da jami’an tsaro wajen da lamarin ya shafa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: