Tsohon gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa babu shakka Jam’iyyar PDP ce za ta karbe ragamar Najeriya a zaben shekarar 2027 mai zuwa.

Tambuwal ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ƙaddamar da raba kayan tallafin Azumi ga Mabukata a jihar.
Kazalika Tambuwal ya ce yana da yakinin cewa a zaben na 2027 PDP ce za ta samu nasara akan Jam’iyyar APC mai mulki a yanzu.

Tambuwar ya ce a baya an kwace mulki daga hannun Jam’iyyar, amma kuma a wannan lokaci sun shirya tsaf don dawo da mulki hannun Jam’iyyarsu.

Acewar Tambuwar Jam’iyyar PDP tun daga kan matakin Jiha, da tarayya sun shirya raba buhunan shinkafa da sauran kayan abinci ga matasa da mata domin tallafa musu a watan na azumi.
Aminu Tambuwal ya kuma mika godiyarsa ga shugaban jam’iyyar PDP ta Jihar da harma da sauran shugabanni ta bisa jajircewarsu wajen ganin sun Karfafa jam’iyyar da kuma hada kan ‘ya’yanta, inda ya ce jam’iyyar PDP, jam’iyya ce mai karfi da hadin kai,
da ke shirin karbe mulki a hannun APC.