Fadar shugaban Kasa ta ce shugaban Kasa Bola Tinubu ya mayar da hankali ne akan kyautata rayuwar ‘yan Najeriya ba zaben shekarar 2027 da ke tafe ba.

Hadimin shugaba Tinubu kan sadarwa Sunday Dare ne ya bayyana hakan ta cikin wata wallafa da ya fitar, ya bayyana cewa ‘yan Najeriya za su ga irin nasarorin da ci gaban tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ta samar zuwa karshen mulki.

Bare ya bayyana cewa shugaban Kasa Bola Tinubu ko kadan bai damu da zaben shekarar 2027 ba, ya mayar da hankali ne kawai akan samarwa da Najeriya ci gaba mai dorewa.

Bugu da kari ya ce shugaba Tinubu ya damu matuka da sauye-sauyen da ya samar da yake fatan za su zamto farin ciki ga ‘yan Kasar.

Sunday Dare ya kara da cewa tun a yanzu a fara gani alamomi akan ci gaban gwamnatin ta Tinubu, duba da yadda farashin kaya ke sauka, ya yin da kasuwanni ke kara habaka da kuma harkokin shige da fice na kayayyaki, tare da zuba hannun Jari da ya kai naira biliyan 50.

Leave a Reply

%d bloggers like this: