Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana cewa gwarzon musabakar karatun Alkur’ani mai tsarki a Jihar Katsina Abdulsalam Rabiu-Faskari da mahaifinsa da kuma dan uwansa da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su, suna nan da ransu a hannun ƴan bindiga ba tare da sun kashe su ba.

Kwamishinan yada labarai da al’adu na Jihar Bala Salisu Zango ne ya bayyana hakan a jiya Juma’a a zantawarsa da manema labarai a Jihar.
Kwamishinan ya ce maharan sun nemi naira miliyan 30 a Matsayin kudin fansa kafin sakinsu.
Zango ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun yi garkuwa da su ne akan hanyar Faskari zuwa ‘Yankara da ke Jihar, bayan karramawar da gwamnan Jihar Malam Umar Dikko Radda ya yi masa.

Kwamishin ya kara da cewa gwamnatin Jihar ta samu labarin wani sakon jaje da ake yadawa wanda mai bai’wa gwamnan jihar Kebbi shawara kan harkokin yada labarai ya sanya wa hannu, da ta bayyana cewa ƴan bindiga sun hallaka gwarzon na Najeriya Abdussalam Rabiu-Faskari.

Kwamishinan ya bayyana godiyarsu ga gwamnatin Jihar Kebbi, inda ya ce amma Rabiu-Faskari da mahaifinsa da kuma ɗan uwansa suna nan da ransu a hannun ƴan bindigar ba su kashe su ba.
Zango ya bayyana cewa gwamnatin Jihar ta Katsina za ta yi dukkan abinda ya dace wajen ganin an tseratar da su daga hannun ‘yan bindigar, tare da kara kaimi akan magance matsalar rashin tsaron da ya addabi Jihar.