Shugaban ƙasar Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, babu wata niyya ko shiri na sauƙaƙa haraji akan ma’adanan Steel da kuma Aluminium sakamakon barazanar kasuwanci da ƙasar ke fuskanta daga takwarorinta.

Tun a watan Janairu ne dai shugaba Trump ya sanya haraji ga abokan kasuwanci da kuma masu shiga da kayayyaki, ciki har da ma’adanan Steel da kuma Aluminium.

Trump ya yi hakan ne dai da niyyar juya akalar ƙara samun kuɗi, da kuma tsoron kar shirye-shiryensa su jefa ƙasar cikin mashashsharar tattalin arziki.

Donald Trump ya shaidawa manema labarai cewa, bashi da niyyar cire tsarin harajin akan wasu keɓaɓɓun abubuwa.

Inda ma ya kuma ƙarfafa tunanin ruɓanya tsarin harajin nan da 2 ga watan Afrilu, dan magance matsalar kasuwanci da kuma sauran matsalolin a ɓangaren.

Trump ya ce zuwa yanzu ƙasar ta samu biliyoyin daloli da tsarin, kuma nan da watan Afrilun za su kuma samun kuɗaɗe masu yawan gaske.

Leave a Reply

%d bloggers like this: