Wani masanin tattalin arziki Farfesa Pat Utomi ya soki shugaba Bola Tinubu bisa ayyana dokar ta baci da ya yi a Jihar Rivers.

Utomi ya bayyana hakan ne a yau Juma’a a yayin wata hira da Channels Tv.

Utomi ya ce babu wani dalili da zai sanya sai an dauki matakin sanya dokar ta baci a Jihar ba.

Acewarsa Farfesa Utomi rikice-rikicen siyasa da ke faruwa a Jihar ta Rivers bai kai ga sai an ayyana dokar ta-baci ba, duba da cewa duk harin da ‘yan bindiga suke kai wa a bututun mai a Jihar ba a taba sanya dokar ta baci ba sai a yanzu.

Sannan masanin ya kuma kalubalanci shugaba Tinubu kan rashin sanya dokar ta-baci a Jihar Legas a bayan rikici ya barke a tsakanin shugaban Majalisar Dokokin Jihar Mudashiru Obasa da wasu ‘yan majalisar Jihar.

Har ila yau ya ce akwai takaici ganin yadda ake kokarin rusa dimokuradiyyar, inda ya kalubalanci Majalisar Tarayyar Ƙasar kan amincewa da ayyana dokar ta bacin a Jihar ta Rivers, kuma hakan cin zarafi ne ga ‘yan Najeriya.

Wannan dai na zuwa ne bayan da shugaba Bola Tinubu ya sanya dokar ta baci a Jihar ta Rivers a ranar Talata, tare da dakatar da gwamnan Jihar Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa da kuma Majalisar dokokin Jihar bisa rikicin da yaki ci yaki cin yewa a Jihar.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: