Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaron Jihar, sun dauki matakin dakatar da hawan sallah da aka saba yi duk shekara a Jihar.

A wani taron manema labarai da aka gudanar a hedkwatar ‘yan sanda ta Kano da ke Bampai a yau Juma’a, Kwamishinan ‘yan sandan rundunar Ibrahim Adamu Bakori ya ce an hana hawan ne don tabbatar da zaman lafiya a Jihar.

Bakori ya ce sun dauki matakin ne bisa samun rahotonnin tsaro da kuma tattaunawa da gwamnatin Kano da masu ruwa da tsaki a bangaren tsaro, domin tabbatar da zaman lafiyar al’ummar jihar.

Bakori ya kara da cewa rundunar za ta aike da jami’anta a sassan jihar domin tabbatar da ganin an bi doka da oda kafin sallah da kuma lokacin bukukuwan sallar.

Kwamishinan ya kuma bukaci al’ummar jihar da su gudanar da sallar cikin kwanciyar hankali, ba tare da tashin hankali ba.

Bakori ya ce an kuma hana hawan doki don yin kilisa, ko tsren motoci, ko kuma tukin gangaci, da dai sauran ayyukan da suka sabawa doka.

Sannan rundinar ta bukaci al’umma da su kai rahoton dukkan wani abu da ba su gamsu da shi ba ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: