Sanata mai wakilar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa Sanata Ali Ndume ya soki nade-naden mukamai da Shugaban Kasa Bola Tinubu ke yi a Kasar.

Ndume ya bayyana hakan ne ta cikin wata hira da aka yi da shi a Tashar Arise TV, yana mai cewa nade-naden sun ci karo da tanadin kudin tsarin mulkin Kasa.
Acewar Ndume mukaman da ake bayarwa a gwamnatin shugaba Tinubu ko kadan ba su cika tanadin sashi na 14 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya ba na shekarar 1999 ba.

Sanatan ya ce kudin tsarin mulkin Kasa ya bayar da damar kowanne yanki a bashi damar wakilci cikin gwamnati.

Ndume ya kara da cewa ya zama wajibi a dunga duba doka a nade-naden da ake yi, yana mai cewa matukar aka ci gaba da tafiya ba tare da yin duba ga kudin tsarin mulkin Kasa ya tana ba, hakan ka iya haifarwa da Kasar Matsala a nan gaba.
Kazalika ya ce ‘yan majalisa na da hakkin sanya idanu akan dukkan ayyukan da shugaban Kasa yi, tare da yi masa gyara a dukkan lokacin da aka samu wani kuskure akan doka, yana mai bayyana cewa wannan shi ne manufar kasancewarsu a matsayin majalisar dokokin Kasar.
Har ila yau Sanata Ndume ya ce ba ya tsoron dukkan wata barazana daga magoya bayan shugaba Tinubu, inda ya ce ya yi wadannan kalamai ne a matsayinsa na dan Kasa da kundin tsarin mulki ya ba shi damar ‘yancin bayyana ra’ayinsa.
A karshe Sanata Ndume ya bukaci shugaba Tinubu da ya dauki matakin gyara akai tun kafin haifar da rashin jituwa ko riki a Kasar.