Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da wani dalibin jami’ar Tarayya da ke Birnin Kebbi mai suna Augustine Madubiya, bayan sun kutsa kai wani gidan haya na dalibai da ke wajen Jami’ar.

Maharan sun kai harin ne da misalin karfe 3:00 na daren yau Talata a Istijaba Villa da ke Unguwar Jeji a Jihar.
Wasu majiyoyi sun ce ‘yan bindigar su biyar dauke da makamai sun kai hari yankin ne a lokacin da daliban ke kwanciyar waje sakamakon zafi.

Rahotannin sun bayyana cewa bayan zuwan ‘yan bindigan sun bukaci kadade a hannun dalibai, bayan rasa kudaden a hannun daliban suka fara dukansu, tare da yin garkuwa da guda daga cikinsu da ke shekarar karshe a Jami’ar a sashen tattalin arziki.

A yayin harin ‘yan bindigan sun kuma hallaka wani mutum mazaunin Unguwar mai suna Malam Siddi Hussaini, bayan fitowarsa domin duba shanunsa da ke kusa da gurin.
An tabbatar da faruwar lamarin ne bayan wata ziyara da mataimakin shugaban Jami’ar Farfesa Muhammad Zaiyan Umar ya kai gurin, tare da Baturen ‘yan sandan Kalgo da kuma jami’an tsaron farin kaya na DSS na Kalgo.
Farfesa Zaiyan Umar ya shaidawa daliban cewa jami’ar za ta tabbatar da ganin ta dauki matakin tsaro a yankin.
Farfesa Zaiyan ya kuma bukaci gwamnatin Jihar da sauran hukumomin tsaro da su sanya hannun wajen ganin an kubtar da dalibin tare kuma da bai’wa jami’ar tsaro mai kyau.