Gwamnan jihar Borno Fafesa Babagana Umara Zulum ya bayyana takaicinsa kan yadda hare-haren Mayakan Boko Haram ke nakasa Jihar ta hanya kai’wa jami’an sojoji hare-hare da kuma kwace wasu daga cikin Yankunan Jihar.

Farfesa Zulum ya bayyana hakan ne a yau Talata a yayin wani taron kwamitin tsaro da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar.
A yayin jawabinsa gwamna Zulum ya bayyana damuwarsa kan sabbin hare-haren Mayakan na Boko-haram, da kuma yin garkuwa da mutane a cikin yankunan kullum yaumin, ba tare da yin adawa da hakan ba, duk da cewa Jihar na samun nakasu a daga wasu yankunan Jihar, inda ya ce Jihar na fuskantar barazanar sake fadawa cikin tashin hankali..

Acewar Zulum gwamnatin Jihar na iya bakin kokarinta wajen ganin ta tallafawa jami’an tsaron soji, da sauran hukumomin tsaro a yaki da suke yi da mayakan na boko-haram da dukkan wasu batagari a Jihar.

Zulum ya kara da cewa tallafawa hukumomin tsaro da gwamnatinsa ta yi, hakan ya sanya aka fara samun zaman lafiya a cikin shekaru uku da suka gabata.
Sai dai Zulum ya ce abin damuwar shi ne yadda hare-haren ya nakasa sansanonin soji da dama musamman a yankunanWulgo, Sabon gari, Wajirko da dai sauransu, ya na mai cewa ‘yan ta’adda sun fara samun nasara akansu, wanda hakan abu ne mai muhimmanci da ke buƙatar yin zama akansa.
Acewar Zulum shekaru uku da suka gabata zuwa yanzu sannu a hankali zaman lafiya ya fara samuwa a Jihar ta Borno, inda ya ce a halin yanzu kuma lamarin ya canja a cikin ‘yan kwanakin nan.
A yayin jawabin na Zulum ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta aike jiragen yaki masu saukar ungulu, da kuma sabbin jirage marasa matuka domin tallafawa sojojin a guraren da ake fama da matsalar.
Zulum ya ce duk da yabawa kokarin jami’an sojojin Kasar dana ‘yan sanda da kuma jami’an DSS kan kiyaye doka da oda a Jihar, ya ce ya zama wajibi su faɗi gaskiya, da kuma duk nasarorin da aka samu zuwa yanzu za su zama na banza.
Gwamnan Zulum ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta kara akimi waje ganin yankin Arewa maso gabashin kasar ya samu kulawar da ta dace.