Gwamnan Jihar Filato Caleb Muftwang ya nuna damuwarsa bisa yadda matsalar rashin tsaro ke kara ta’azzara a wasu yankunan Jihar, inda ya ce a halin yanzu ‘yan ta’adda sun mamaye kimanin Garuruwa 64 na Jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yau Labara, ta cikin shirin Politics day na gidan Talabijin na Channels.
Gwamna ya danganta matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a Jihar akan ‘yan ta’adda, yana mai cewa akwai masu daukar nauyin hare-haren.

Caleb ya bayyana cewa abu mafi muhimmanci shine, hukumomin tsaro su mayar da hankali akan gano wadanda ke daukar nauyin ‘yan ta’addan, duba da cewa ba a san ko su wanenen ba.

Bugu da kari ya ce garuruwa da a baya-bayan nan aka kai’wa hare-hare na daga cikin yankunan da suka fuskanci hare-hare a shekarar 2023, inda mazauna garuruwan suka koma muhallansu.
Gwamnan ya bayar da misali da cewa a shekarar ta 2023 mahara sun kai hari Kauyen Ruwi, wanda ya yi ajalin mutane 17, duk da haka mazauna yankin suka sake gina muhallansu.
Acewar akalla shekaru kusan Goma da aka kwashe ana wannan ta’addanci shi yake nuna cewa akwai masu daukar nauyinsu, domin kawo karshen mutane a doran Kasa.
Gwamna Caleb ya ce garuruwan da ‘yan ta’addan suka mamaye na a tsakanin ƙananan hukumomin Bokkos, Barkin Ladi, da Riyom, inda suka sauya musu suna bayan sun kwace su, kuma a hakan mutane ke ci gaba da rayuwa a cikinsu.
Gwamnan ya yi fatan cewa nan da wani lokaci kalilan hukumomin tsaro za su hada kai domin kawo karshen matsalar.