Ministan Abuja Nysom Wike ya halarci taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP dangane da ficewar da ake yi a cikin jam’iyyar.

Taron da ya kunshi gwamnonin PDP da sauran masu ruwa da tsaki ana yin sa ne a gidan gwamnan Bauchi da ke Asokoro a birnin tarayya Abuja

Daga cikin waɗanda su ka halarci taron akwai tsaffin gwamnonin jam’iyyar PDP waɗanda ke cikin jam’iyyar.

Masu ruwa da tsakin ana tsammanin za ku ma su tattauna batun haɗaka da wasu ke shirin yi da kuma babban taron jam’iyyar na ƙasa.

Daga cikin gwamnonin jihohin da su ka halarta akwai na Bauchi Bala Muhammad, Oyo Seyi Makinde, Filato Caleb Mutfwang, Osun Ademola Adeleke, Adamawa Ahmadu Fintiri, Wnugu Peter Mbah da Zamfara Dauda Lawal Dare.

Tsaffin gwamnonin da su ka halata akwai Ahmed Makarfi na Kaduna, Bukola Saraki na Kwara, Ganriel Suwang na Benue, Babangida Aliyu na Niger, Aminu Waziri Tambuwal na Sokoto da Samuel Ortom na Benue.

Sauran su ne Olezir Ikpeazu na Abia, Serake Dickson na Bayelsa, Liyel Imoke na Cross Rivers Achike Udenwa na Imo, Ifeanyi Ugwanyi na Enugu, Ibrahim Shekarau daga Kano da Olagunsoye Oyinlola na Osun da sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: