Ahmad Sulaiman Abdullahi


Jami’an ƴan sandan Najeriya sun samu nasarar damƙe masu safarar makamai huɗu a Jos, jihar Plateau ɗauke da bindigogin AK47 guda hamsin da bakwai (57).

Kakakin hukumar, CSP Muyiwa Adejumobi, a jawabin da ya fitar ranar Alhamis yace matasa huɗu masu matsakaici shekaru kuma duka mazauna Jos na wannan harkar.
Ya ƙara da cewa, an kama su ne sakamakon harin sirri da akai musu.
Yace: “Jami’in rundunar FIB-IRT a harin sirri, sun damke wasu dilolin makamai huɗu kuma sun kwato bindigar AK47 guda 57 da dinbin harsasai a Jos da wasu jihohi.”
“Matasan masu suna Hamza Zakari (aka Hamzo) ɗan shekara 20, Abubakar Muhammed (aka Fancy) ɗan shekara 22, Umar Ibrahim ɗan shekara 25 da Muhammed Abdulkarim (aka Ɗan-Asabe) ɗan shekara 37, duka mazauna Jos.”
Ya ƙara da cewa matasan sun amsa laifin da ake zarginsu da shi kuma an gano suke dillancin makamai wa ƴan bindiga dake addabar al’ummar yankin.
A cewarsa, an ƙaddamar da bincike don bibiyan abokar harkarsu da wadanda suke sayarwa makamai.