Wasu ‘yan bindiga sun hallaka mutane shida tare da yin garkuwa da ma’aikata uku a lokacin da su ka kai hari wani kamfanin sarrafa tasa da ke garin Ajaokuta da ke Jihar Kogi.

Wata majiya daga Jihar ta bayyana cewa ‘yan bindigan sun kutsa kai cikin kamfanin ne da misalin karfe bakwai na daren Jiya juma’a inda zuwan su ke da wuya su ka hallaka ma’aikata hudu da ke cikin mota.

Shima wani daga Jihar wanda lamarin ya faru akan idonsa ya bayyana cewa maharan sun shiga yankin a cikin wasu motoci guda biyu inda su ka farwa ma’aikatan kamfanin.

Daga cikin wadanda ‘yan bindigan su ka hallaka ciki harda ‘yan sanda biyu a lokacin da su ka yi musayar wuta da maharan.

Ya ƙara da cewa yayin da ‘yan bindigan su ka kai hari a lokacin ne ma ‘aikatan su ke nufin tafiya masaukin su.

Kwamishinan yada labaran gwamnatin Jihar ya bayyana cewa gwamnatin ta yi allah wa-dai da harin ‘yan bindigan.

Kwamishinan ya kara da cewa gwamnatin za ta jajirce domin ta kubtar da wadanda aka yi garkuwa da su tare da kamo wadanda su ka yi aika-aikar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike akan lamarin tare da ƙoƙarin kuɓutar da mutanen.

Leave a Reply

%d bloggers like this: