Rundunar yan sanda a jihar Ekiti ta kama mutanen da su ka saci takalma 220 aa jihar

Mutanen biyu Olamide da Michael an kama su bisa zargin fasa shaguna da wasu gidaje tare da sace takalma a babban birnin jihar.
Mai magana da yawun ƴan sandan jihar Sunday Abutu ne ya sanar da haka a wata sanarwa da ya sanyawa hannu.

Ya ce mutanen sun fasa gidaje 16 da kantina a Ado Ekiti babban birnin jihar.

Ya ƙara da cewa akwai wasu guda uku da su ka tsere bayan kama mutanen biyu.
Daga cikin kayayyakin da mutanen su ka sata akwai takalma 220 barasa, kayan sakawa na maza da mata da kayan lantarki sai kayan abinci.
Kakakin ƴan sanda a jihar ya ce su na ci gaba da gudaanar da bincike kuma da zarar sun kammala za su gurfanar da mutanen da ake zargi a gaban kotu.
