Kamar yadda Wani Kwararren likita kuma masani a bangaren magunguna da zamantakewar Iyali mai suna Dakta Ugwele dake Asibitin Tarayya a jihar Abia.
Inda Yace Maza masu Shekaru Hamsin (50) zuwa sama su sukafi fuskantar kamuwa da cutar kansar mafitsara.
Dakta Ugwele ya bayyana hakan ne ga manema labarai.
Kamfanin dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta rawaito cewa Binciken Ugwele ya nuna cewa matsalar kansar mafitsara sananna ce ga maza masu yawan shekaru, kuma mafi yawanci maza da suke sama da shekaru Hamsin (50) na da irin wannan alamar ciwon.
Yace wannan ciwon nada matukar matsala a rayuwa saboda rashin fahimtar ciwon da mutane basuyi ba.
Ya ƙara da cewa rashin fahimtar matsalar ya jawo dubban jama’a rasa rayuka sakamakon rashin baiwa ciwon kula da neman hanyar magance shi.
Dakta Ugwele yace matsalar kansar mafitsara tana bayyana kanta ne ta hanyar kumburan ƴaƴan maraina shine ake kiranshi da kansar Mafitsara.
Dakta Ya ƙara da cewa, Manyan Alamun da ke tattare da Kansar mafitsara sune: Yawan fita Fitsari, Rashin ƙare fitsari gaba ɗaya lokacin yinshi, sannan ɗigan Fitsari lokacin da yake zuwa.
Dakta Ugwele ya bada shawara ga duk wanda yaga irin wannan alamu to ya hanzarta zuwa Asibiti don duba lafiyarsa.


