An fara kiraye-kiraye na adakatar da batun sake fasalin naira.

Wata kungiya mai suna concern northern forum tayi kira da a dakatar da canza fasalin takardar kudi, Wanda aka shirya canza fasalin naira 200 da 500 da kuma naira 1000, inda tace matakin zai yi illa ga tattalin arzikin kasa.
Babban bankin Najeriya CBN ya sanar da cewa zai sake fasalin takardun kudi daga ranar 15 ga watan Disamba.

Da yake mayar da martani a wata sanarwa a yau Alhamis a birnin Kaduna mai magana da yawun kungiyar Abdulsalam Kazeem, yace sake fasalin zai yiwa darajar naira illa.

Ya bayyana cewa sunyi kira da a dakatar da kudurin ne duba da cewa farashin naira zuwa dala da fam ya sanya naira ta rasa darajarta.
Yayi kira daa samar da manya-manyan tsare-tsare na tattalin da zasu karfafa naira idan aka kwatatta da dalar Amurka da Fam na kasar Ingila.
Mai magana da yawun kungiyar yace tattalin arzikin Nigeria ya karye, kuma darajar naira ta yi kasa sosai, don haka sake fasalin takardun kudin zai jawowa gwab
Mnati asarar makudan kudade, kuma kudaden talakawa za’a diba ayi aikin a cewarsa.
