Shaharraren ɗan kwallon ƙafa, dake ƙungiyar Juventus Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa Pep Gurdiola shine kaɗai zai iya kai ƙungiyar da samun Nasarar lashe kofin zakarun turai.
Ronaldo ya bayyana hakan ne tun bayan da ƙungiyar sa ta juventus ta gaza kaiwa matakin daf da na ƙarshe a gasar cin kofin zakarun turai, wanda ƙungiyar Ajax ta lallasa ƙungiyar ta juventus.
Gurdiola dai shine Mai horar da ƙungiyar Manchester City dake Ƙasat Ingila, wanda ya lashe kofin Primiya ɗaya, da wasu kofunan jikin gida guda biyu, tun bayan da yaje ƙungiyar a shekarar 2016, bayan ya bar ƙungiyar Barcelona dake ƙasar Spaniya.
Yanzu haka dai ƙungiyar juventus na shirin fara zawarcin shi Pep Gurdiola.
Wanda zai maye gurbin Macx Allegri.


