A kalla 32 cikin mutane 200 da aka yi garkuwa dasu daga anguwar Randa cikin karamar hukumar Maru na jihar Zamfara ne suka rasa rayukansu a hannun masu garkuwa da mutane.

Sarkin Mutumji, Abdulkadir Abdullahi ne ya bayyanawa manema labarai a yammacin Litinin.
Haka zalika, Abdullahi ya ce an saki sauran 200 da aka sace bayan biyan kudin fansa.

Manema labarai sun ruwaito yadda ‘yan ta’addan wadanda mabiyan gawurtaccen shugaban ‘yan ta’addan nan, Lawalli Damina, suka sace gaba daya mazan yankin Randa saboda batan bindigunsu.

An yi garkuwa dasu ne bayan musanta sanin inda bindigun biyu da suka bace a yankin suke.
An gano yadda bindigun suke mallakin mayaka biyu na shugaban ‘yan ta’addan wadanda wasu tawagar ‘yan bindiga suka halaka bayan sun yi rikici saboda budurwa a yankin.
Sai dai, Abdullahi ya ce an biya N6 miliyan ga ‘yan ta’addan yayin da za a biya N24 miliyan daga baya bayan an saki wadanda aka yi garkuwan dasu kamar yadda aka yi alkawari.