Dan Takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar APC Asiwaju Bola Tinubu yayi zargin cewa, matsalar karancin man fetir da tsadarsa a kasar nan sa hannu ne masu yi masa makarkashiya.

Ya bayyana hakan ne a yau Laraba a wajen gangamin yakin neman zabensa, da ya wakana a filin wasa na MKO Abiola a Abeokuta.

Da yawan yan Najeriya dai suna ta kokawa akan rashi da tsadar man fetir, in da ake siyan kowacce Lita akan Naira 270 zuwa Naira 400.

Jaridar Punch ta ruwaito Dan takarar yana cewa, akwai shirin na wadansu masu yin makarkashiya a zabe mai zuwa.

Tinubu bai bayyana mutanen ba amma yayi zargin su akan rashin Mai, da kuma boye kudade Dan dakatar da aiwatar da zabe.

Ya kuma kara da cewa sun boye mai kuma sun boye kudade, amman sune kadai suka San dalilinsu Na yin hakan.

Ya kuma fadi cewa idan suna so ma su canza tawadar jikin kudin, babu abinda zai hana shi yin nasara a zabe sannan jam’iyyar PDP ta sha kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: