Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da shugaban hukumar zabe na ƙasa yayin da ya rage kwanaki uku gabanin babban zabe a ƙasar.

 

Ganawar ta bazata ta faru ne a yau bayan da shugaban kasar ya bukaci tattaunawa da shugaban hukumar zabe Farfesa Mahmud Yakubu.

 

A yayin tattaunawar shugaba Buhari ya shaidawa shugaban zaɓen cewar ya ƙaddamar da kayan aiki ga jami’an tsaron soji da ƴan sanda da kudinsu ya kai naira biliyan 12.

 

Shugaba Buhari ya ce ya yi duk mai yuwuwa wajen ganin an gudanar da zaɓe lafiya, kuma ganawar tasu na daaga cikin tattauna yadda zaɓen zai gudana ba tare da wata matsala ba.

 

A na sa ran gudanar da babban zaben shugaban kasa daa ƴan maajalisar wakilai da majalisar dayyawa raanar Asabaar mai zuwa.

 

Shugaba Buhari yau Laraba ya jagoranci zaman majalisar zartarwa ta ƙasa wanda ya samu halartar shugabannin tsaro da wasu daga cikin ministocinsa.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: