A yayin da ya rage kasa da kwana daya a gudanar da zaben gwamnoni da ‘yan majalisun Jihohin Najeriya ,hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta aike da jami’an 200 zuwa Jihohin Kano Katsina da Jigawa domin dakile masu sayan kuri’u a lokacin zabe.

 

Kwamandan hukumar Shiyya na Jihar Kano Mr Faruk Dogondaji ya bayyana hakan a lokacin da ya ke ganawa da kamfanin dillanci labarai na kasa NAN a ranar Alhamis.

 

Kwamandan ya ce sun tura jami’an nasu da su ka yi na daya daga cikin aikin hukumar domin ganin an tabbatar da an gudanar da zabe cikin nutsuwa da gaskiya a shiyyoyin.

 

Dogondaji ya kara da cewa sun aike da jami’ai 50 Jihar Kano 50 Jihar Katsina 50 kuma Jihar Jigawa yayin da sauran 50 din kuma ta aike da su filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano tare da na Umaru Musa ‘yar Aduwa da ke Jihar Katsina.

 

Mr Faruk ya bayyana cewa tura jami’an guraren zaben zai taimaka wajen ganin an yi sahihin zabe.

 

Sannan ya ce za su isa cibiyoyin tattara sakamakon zabe domin dakile lalata sakamakon zabe daga kananan hukumomi harma da matakin Jiha.

 

Daga bisani ya bukaci iyaye da su hana ‘ya’yansu shiga harkar dabar siyasa domin za a hukunta su idan aka kama masu hannu a ciki

Leave a Reply

%d bloggers like this: