Dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, ya tunatar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa babban hakki ɗaya da ya rataya a wuyansa shine ceto yan Najeriya da ke makale a Sudan.

An ruwaito cewa sama da yan Najeriya 4000 ne suka makale a kasar ta arewa maso gabashin Afrika sakamakon rikicin da ya barke tsakanin rundunar soji da ƴan adawa.


Bangare daya na biyayya ga shugaban hafsan soji, Abdel Fayyah al-Buthan, daya bangaren kuma na biyayya ga Mohamed Hamdan Daglo, mataimakin Shugaban hafsan sojin kuma kwamandan rundunar RSF.
Da farko gwamnatin tarayya ta bayyana hatsarin da ke tattare da kwashe yan Najeriya da suka makale a Sudan saboda tashin hankali da ke kasar.
Ta kuma bayyana cewa za a kwashe yan Najeriyan da suka makale nan ba da Jimawa ba bayan kafa wani kwamiti karkashin jagorancin ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama.
Sai dai kuma, a wasu jerin wallafa da ya yi a shafinsa na twitter, a ranar Lahadi, 23 ga watan Afrilu, Obi ya bayyana cewa yana daya daga cikin hakokin gwamnatin tarayya ta ceto yan Najeriya da suka makale.
Yayin da yake nuna tsananin damuwa game da ci gaban, Obi ya yi kira ga gwamnatin Buhari da ta yi amfani da kowace hanya wajen ceto yan Najeriya sama da 4000 da suka makale a Sudan.