An zartar wa da wani mutum hukuncin kisa a kasar Saudiyya ranar Talata saboda kai wa ’yan sanda hari.

Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ta ce an yanke wa Anwar bin Jaafar bin Mahdi al-Alawi hukuncin kisa ne bayan samun sa da laifin bude wa wani ofishin ’yan sanda wuta.

Haka kuma an same shi da laifin bayar da mafaka ga wani wanda jami’an tsaro ke nema kan mallakar makami ba bisa ka’ida ba.

Sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ta fitar ta kara da cewa kisa shi ne hukuncin duk wanda aka samu da irin wannan laifi.

Abaya hukumar ta sanar da cewa adaina kai hari wurare kamar yadda su ka sanar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: