Tsohuwar ministar Man Fetur a gwamnatin tsohon shugaban Kasa Goodluck Jonathan Diezani Alison Madueke ta shigar da karar hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Kasa Zagon Kasa ta EFCC da babban lauyan gwamnatin tarayya Abubakar Malami a gaban Kotu.

jaridar Daily trust ta rawaito cewa tsohuwar ministar ta shigar da su kara gaban Kotun ne domin su biyata diyyar naira biliyan daya sakamakon bata mata suna da su ka yi.


A yayin shigar da karar wanda lauyan ta Mike Ozekhome SAN ya shigar Diezani ta bukaci da Kotun ta tilastawa hukumar ta EFCC ta rubuta mata sakon ban hakuri a cikin akalla manyan Jaridu guda uku na Najeriya.
Diezani ta bayyana cewa hukumar za ta wallafa sakon ban hakuri ne a Jaridun The Punch The Sun da kuma This day, tare da wallafawar a cikin kwanaki bakwai da yanke hukuncin Kotun.
Tsohuwar Ministar ta kara da cewa rubuce-rubucen da hukumar ta EFCC ta yi a kanta ta yi su ne da nufin bata mata suna da cin zarafin ta.