Rundunar sojin Najeriya Sun yi nasarar gano wani gida da ake siyar da jarirai a jihar Abia.

Jami’an tsaron runduna ta 14 da ke Ohafia ne su ka samu nasarar bankaɗo gidan wanda aka ajiye masu juna biyu da nufin su haihu a siyar da jariran.

An kubutar da mata guda 22 kuma daga ciki akwai 21 da su ke da juna biyu, sannan an gano jarirai guda biyu a gida.

Sannan jami’an sun samu nasarar gano abubuwan amfanin yau da kullum a gidan ciki har da kayan abinci.

Jami’an sun ce sun kai sumame gidan ne bayan da su ka samu bayanan sirri a kan gidan wanda ake siyar da jaridan don yin tsafi da su.

A na zargin an dade ana amfani da gidan wajen aikata laifin bayan da ake yawan ganin sassan jikin mutum a kusa d gidan.

Tuni jami’an su ka miƙa mata da jariran da su ka kubutar zuwa ga gwamnatin jihar Abia.

Leave a Reply

%d bloggers like this: