Kungiyar gwamnonin jihohin kasa Najeriya sun amince da cire tallafin man fetur da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu yayi.

Hakan ya fito bayan wata ganawa da gwamnonin su ka yi da shugaban kasan Najeriya Bola Tinubu a fadarsa dake babban birnin tarrayyar Abuja a jiya Laraba.


Kamar yadda shugaban kungiyar gwamnonin ya bayyana kuma gwamnan jihar kwara Abdurazak Abdurahman cikin bayanansa da yayi.
Ya ce sun amince da cire tallafin man fetur din da aka yi .
Sannan ya ci gaba da cewa suna mai fatan hakan zai kawowa kasar ci gaba.
A ranar 29 ga watan mayu shugaban kasar Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa ya cire tallafin wanda ake bai wa bangaren mai a kasar.
Abin da ya jawo ce-ce-ku ce a kasar har ta kai ga kungiyoyin kwadago suka shirya shiga yajin aiki, sai dai bayan wata ganawa da suka yi tare da cimma matsaya.
Sannan shugaban Tinubu ya bayyana cewa zai karkatar da kudin zuwa wasu fannin don raya kasar.