Kungiyar Kwadago ta Kasa NLC ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta da ta dakatar da shirinta na yunkurin ƙarin kuɗin wutar lantarki da kashi 40 cikin 100 a cikin watan mai kamawa.

Shugaban ƙungiyar Joe Ajaero ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa ya fitar a Abuja, ya ce matakin karin kudin wutar zai Kara wa talakawa matsin rayuwa baya ga wanda su ke ciki a yanzu.
Shugaban ya kara da cewa shirin janye kudin wutar hakan zai nuna halin ko in kula da rayuwar talakawan Najeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa hukumar kula da harkokin wutar lantarki ta Najeriya NERC ta bayyana shirin ta na ƙara kuɗin wutar daga ranar 1 ga watan Yuli shekarar 2023 a matakin gwamnatin na janye tallafin da ta ke biya kan kudin wutar.

A yayin da BBC ta nemi jin ta bakin hukumar mai magana da yawun hukumar Michael Faloseyi ya bayyana cewa ba a bashi umarnin yin magana akan batunnba.
Bayan shirin gwamnatin na janye Karin kudin wutar ‘yan Najeriya da dama sun nuna rashin jin dadinsu akan matakin ƙarin, inda hakan zai haifar da ƙarin matsin tattalin arziki.
Shugaban hukumar ta NLC ya bukaci da gwamnati ta haramta karin kuɗin wutar.
Idan ba a manta ba dai a watan Mayun da ya gabata ne dai gwamnatin ta tarayya ta bayyana matakin janye tallafin man fetur, Wanda hakan ya haifar da ƙaruwar farashin man fetur da sauran kayayyaki a fadin Kasar.
