Daya daga cikin manyan kwamandojin ƙungiyar ISWAP mai suna Kiriku ya rasa ransa bayan wani maciji ya sareshi a dajin Sambisa da ke Jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa Kiriku ya mutune bayan yasha saran maciji mai guba wanda yake da kalar launin ruwan ƙasa a maɓoyarsu da ke a masallacin Agikur cikin ƙaramar hukumar Damboa ranar Talata daga bisani ya mutu a ranar Juma’a.
Masani akan sha’anin tsaro a yankin Tafkin Chadi Zogazola Makama ya ce Kiriku ya mutu ne a dalilin rashin samun kayan aikin da za a duba lafiyarsa.

Kiriku dai na daya daga cikin kwamandojin kungiyar mayakan da ke gudanar da ayyukan ta’addanci a yankunan Jiddari na Chiralia a cikin Timbuktu da kuma tsakanin hanyar Maiduguri zuwa Damboa duk da ke Jihar ta Borno.

Inda su ke kai wa al’umomin yankunan hare-hare harma da jami’an tsaro wanda hakan ya haifar da asarar rayuka dukiyoyin da kuma raba wasu da muhallansu.
Jihar Borno dai na ci gaba da fama da rikice-rikice sama da shekaru Goma.
