Akalla Alhazan Najeriya 13 ne suka rasa rayukansu a hajjin bana, yayin da mutane 41,632 suka kamu da rashin lafiya a Kasar Saudiyya.

Shugaban likitocin Najeriya mai kula da alhazai Dakta Usman Galadima ne ya bayyana haka a ranar Lahadi a garin Makka.
Usman ya ce sun kula da marasa lafiya 25,772 a filin Arfa yayin da suka kula da mutane 15,680 a Makkah da Madinah kafin ranar Arfa.

Usman ya kara da cewa mutane bakwai da suka fito daga jahohi daban-daban ne suka rasa rayukansu kafin Arfa .

Galadima ya ƙara da cewa mutanen da su ka rasa rayukansu sun fito ne daga Jihohi kamar haka Jihar Kaduna 2 Osun 2 Filato 1 Borno 1 Lagos 1 Yobe 1 Benue 1 sai kuma birnin Tarayya Abuja 1.
Kazalika Dr Usman ya ce suma jiragen yawo sun samu mutane uku da suka rasa rayukansu.
Sannan ya yi kira da a dakatar da hana tsoffi da kuma marasa lafiya zuwa gurin jifan shaidan sakamakon cinkoson da ake fuskanta.
A yayin jawabinsa Kwamishinan Hukumar Alhazai ta kasa NAHCON Goni Sanda ya ce za su fara jigilar maniyyata zuwa gida Najeriya a ranar 4 ga watan Yulin da muke ciki zuwa ranar 3 ga watan Agusta.