Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi kira ga ’yan Najeriya da su koma amfani da keke a matsayin hanyar sufuri da nufin kawar da fitar da gurbatacciyar iska da ke gurbata muhalli.

 

Daraktan Gudanarwa na Sufuri da Jigila a Hanyoyi Musa Ibrahim ne ya bayyana hakan a gurin wani taron masu ruwa da tsaki a birnin tarayya Abuja.

 

Daraktan ya ce yin amfani da keken zai samar da karin fahimta da kuma bunkasa amfani da kekuna a tsakanin ’yan Najeriya.

 

A jawabin da Shugaban Kamfanin Ochenuell Mobility kuma mai rajin kare harkokin sufuri mara fitar da hayaki Emannuel John, ya ce alfanun tuka keke ya wuce batun kare muhalli ko hanyar rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli a Kasar.

 

A yayin binciken da hukumar hadakar bunkasa tattalin arziki Kasa OECD ta fitar ya nuna a kowace shekara yawancin kasashen Afirka suna yin asarar kashi 3 cikin 100 na dukiyar da ake samarwa a cikin gida a sakamakon cinkoson ababen hawa.

 

Shugaban kamfanin ya jaddada muhimmancin amfani da tsarin sufuri mara hayaki domin magance wadannan matsaloli a fadin Najeriya.

 

Kiran na zuwa ne a lokacin da ’yan Najeriya ke korafi game da tsadar man fetur a fadin Kasar wanda hakan ya sanya mafiya yawa daga cikin ‘yan Kasar daina amfani da ababan hawan su tun bayan janye tallafin Man Fetur da gwamantin Kasar ta yi.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: