Tashin Bom ya kashe ɗaruruwan Falasɗinawa a asibitin Al-Ahli Al-arabi, wanda yake cike da mutane marasa lafiya, da waɗanda suka rasa matsugunansu, hukumomin lafiya su ka sanar da hakan.

Bom ɗin ya tashi ne sakamakon harin da Isra’ila suka kai a jiya Talata, cikin asibitin da ke yankin Gaza a ƙasar ta Falasɗin.

Harin dai shi ne mafi zubar da jini, tun lokacin da Isra’ila ta fara Ƙaddamar da jefa bama-bamai zuwa zirin Gaza.

Hukumar ma’aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da cewa, harin yayi sanadiyyar mutuwar kimanin mutane 500, inda wasu kuma suka jikkata.

A nata ɓangaren Ƙungiyar Hamas ta ce mafi yawan mutanen da su ka rasa matsugunansu harin Bom ɗin ya shafa, wanda suka haɗar da marasa lafiya mata da ƙananan yara.

Babban mamban Ƙungiyar Hamas Izzat El-Reshiq ya ce, akwai tarin gawarwaki da aka kwashe malale cikin jini a wajen.

Sai dai sojojin Isra’ila sun ce, basu da wata masaniya ko wani rahoto game da harin Bom ɗin.

A gefe guda kuma Ƙungiyar majalisar ɗinkin duniya da suke tallafawa ƴan gudun hijirar Falasɗin sun ce, mutane shida sun mutu a ɓangarensu, yayin kai harin na Isra’ila.

Leave a Reply

%d bloggers like this: