Majalisar wakilan Najeriya ta yanke shawarar shiga tsakani doguwar taƙaddamar da ke wakana tsakanin Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU da gwamnatin tarayya. Akan riƙe musu albashin tsawon watanni takwas.

Yanke shawarar ya biyo bayan gamayyar goyon bayan ƙudurin ƴan majalissu Paul Nnamchi daga jihar Inugu, Aminu Jaji daga Zamfara, Julius Ihonvbere daga Edo, da Lilian Orogbu daga Anambara su ka gabatar a gaban majalisar.
Yayin gabatar da ƙudirin ɗan majalisa Nnamchi ya ce, malaman jami’o’in suka taka muhimmiyar ga ɓangaren ilimin ƙasar nan ta hanyar samar da ilimi, shawarwari da kuma zama madubai abin kallo ga manyan gobe.

Ya ƙara da cewa ƙungiyar ta ASUU babban dandamali ne na ƙwararrun masu ilimi a Najeriya, kuma sun duƙufa kullum wajen bunƙasa ilimi da yin bincike a jami’o’i.

Idan za a iya tunawa dai a shekarar 2022 da ta gabata, Ƙungiyar ta ASUU su ka gudanar da yajin aikin tsawon watanni takwas, sakamakon gaza cika alƙawarin da gwamnatin tarayya ta yi na yarjejeniyar da ke tsakaninsu.
Ɗan majalisa Nnamchi ya ce ƙudurin yajin aikin da malaman suka yi yana nufin shawo kan matsalar da take damun ɓangaren ne, amman ya janyo sakamakon riƙewa malaman da suka yi shi haƙƙoƙinsu na kuɗi.
Ya kuma bayyana cewa malaman jami’o’in sun shiga matsanancin hali sakamakon riƙe musu albashin nasu na watanni takwas, kuma hakan zai shafi rayuwarsu da kuma aikin nasu.