Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Abuja ta tsige Hon Suleiman Wanchiko mai wakiltar mazabar Bida I a jihar Neja.
Kotun mai alkalai mutum uku karkashin jagorancin Mai shari’a Bature Isa Gafai ya ayyana Bako Kasim na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben dan majalisar jihar.
Kotun Daukaka Karar ta tabbatar da cewar karar da dan takarar PDP, Wanchiko ya daukaka bata da inganci.
Mai shari’a Isa-Gafai ya yarda cewa bai kamata a bari Wanchiko ya yi takara a zaben ba kasancewar ya gabatarwa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da takardar bogi.
Wanchiko, ta hannun lauyansa, Aliyu Lemu, SAN, ya tunkari Kotun Daukaka Kara bayan an yi umarnin sake zabe ba tare da shi ba.
Kotun ta yanke hukunci cewa bayan tsige Wanchiko, hukuncin da ya dace shine ayyana Kasim a matsayin wanda ya lashe zaben tare da umurtan hukumar INEC da ta ba shi takardar shaidar cin zabe.


