Jami’ar kimiyyah da fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil, ta warware bayani game da tsaikon da aka samu dangane da rajistar fara karatu na sabon zangon karatu.

Bayanin wanda ya fito ta bakin Jami’in hulɗa da jama’a na jami’ar Sabo Nayaya, a wata tattaunawarsa da jaridar Daily News 24 a jiya Talata.

Nayaya ya ce, tsaikon ya samu ne sakamakon shirye-shiryen da ayyukan da hukumom jami’ar suke yi, na fara sabuwar kakar zangon karatu. Shi ne dalilin da yasa ɗalibai basa samun damar shiga manhajar makarantar don yin rajistar fara sabon zangon.

Kuma ya ƙara da cewa, hukumar makarantar tuni ta saki jadawalin fara sabon zangon karatu, kuma nan ba da jimawa ba karatu zai kankama a makarantar.

Nayaya yayi tsokaci ne dai game da game da jita-jitar da ake ta yaɗawa cewa, jami’ar ta ƙi bayar da damar yin rajista a shafin makarantar na yanar gizo ne, saboda ragin kaso 50 cikin 100 na kuɗin makaranta da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf yayi.

Wani ɗalibin jami’ar ya shaidawa wakilin Jaridar Daily News 24 cewa, ƙwarai da gaske har yanzu jami’ar ba ta buɗe shafinta na yanar gizo ba. Kuma ba su faɗi dalilin hakan ba a hukumance.

Leave a Reply

%d bloggers like this: