Gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya sanya hannu a kan kudirin dokar samar da jami’an tsaron al’umma a Sokoto.

A ranar 21 ga watan Disamba ne majalisar dokokin jihar ta amince da kudirin gwamnan na kafa jami’an sintiri a jihar.
Da yake rattaba hannu kan kudirin dokar a gidan gwamnati, Aliyu ya ce gwamnatinsa ta kafa rundunar tsaron don tallafawa kokarin gwamnatin Bola Tinubu na samar da isasshen tsaro ga al’umma.

Ya kara da cewa jami’an tsaron al’ummar ba kishiyar ‘yan sanda bane.

Ya yi kira ga sauran jami’an tsaro da su ba rundunar da ya kaddamar goyon baya domin an samar da ita ne don su taimaka a yunkurin ganin an samu zaman lafiya.