Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ba da umarnin biyan ma’aikatan gwamnatin jihar da na kananan hukumomi albashinsu wata guda a matsayin kyautar karshen shekara.

A yau Juma’a Gwamna Lawal ya umarci ma’aikatar kudin jihar ta biya alawus din da ake kira 13th Month ba tare da bata lokaci ba.

Shugaban ma’aikatan jihar, Ahmed Liman ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Juma’a.

Karo na farko ke nan da ma’aikatan Zamfara za su shaida irin wannan tagomashi, a cewar kakakin gwamnan, Sulaiman Idris.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya ruwaito Sulaiman Idris na cewa gwamnan ya amince da biyan ma’aikatan jihar da na kananan hukumomi alawus-alawus na karshen shekara ne da nufin kara musu kwarin gwiwa da kuma ba su tallafin kudi a lokacin hutu.

Wannan matakin shaida ne kan muradinsa na aiwatar da tsare-tsare da za su inganta yanayin aiki, kara albashi, da samar da damar ci gaban sana’o’i ga ma’aikatan gwamnati.

Ya ce biyan albashin 13th Month  daya ne daga cikin tsare-tsarensa na karfafa gwiwar ma’aikata da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar Zamfara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: