Iyayen daliban jami’ar tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara, sun kai kukansu zuwa gaban gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Wadannan Bayin Allah sun roki gwamnatin tarayya ta ceto ‘ya ‘yansu da yan bindiga suka sace kafin su zama tarihi.

Iyayen sun nemi gwamnati ta tattauna da ‘yan bindigan da suka dauke ‘ya ‘yansu kamar yadda aka yi da irinsu a lokacin Boko Haram.

A jiya Alhamis ne iyayen suka yi wannan roko bayan bidiyo ya bayyana, inda aka ji ‘yan ta’addan suna barazanar kashe yaransu.

Idan har ba a iya biya masu bukatunsu ba ‘yan bindigan sun yi alkawarin hallaka wasu daga cikin ‘yan matan da su ka dauke.

Jaridar ta ce ‘yan bindigan sun samu wani shugaba wanda yake rike da daliban makarantar da su ka rage bayan an ceto wasu a baya.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: