Majalisar Dinkin duniya ce ta ware Dukkanin Ranar 26 na watan agusta a matsayin Ranar Hausa.

Harshen hausa dai na Daya daga cikin Harsunan da suke dada Tumbatsa a duniya, ba ma iya Najeriya kawai ba.
Harshen hausa ta samu Karbuwa a duniya idan akayi la’akari da hanyoyin zamani na isar da sakonnin Fadakarwa da ilmantarwa da ake da yaren hausa.

A baya bayannan ne dai kasar Saudiya Ta amince da a rika Fadakarwa da yaren hausa a masallacin Annabi dake Madina.
Wannan na nuni da da cewa Harshen hausa na yaduwa da kuma Karbuwa idan akayi la’akari da yadd Turawan mallaka suka rika amfani dashi wajen isar fa sakonnin da kuma mu’amalar zamantakewa.

Anyi amfani da Harshen hausa wajen isar da sakonnin sojojin da aka kwasa daga arewacin Najeriya zuwa Kasashen da ake gudanar da yakin duniya na Daya.