Rundunar yan sandan jihar Kebbi ta tabbatar kama wata mata da ake kira da suna Auta Dogo da laifin hada baki da wasu mutane biyu domin su kashe mijinta mai sun Abdullahi Shaho.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Garba Danjuma shine ya bayyana hakan ga manema labarai a Birnin Kebbi.

Kwamishinan ya ce Auta ‘yar asalin kauyen Sabongari ne dake karamar hukumar Badugo sannan shi mijinta Mai suna Shaho dan kauyen Tungar Bature ne.

Ya ce Auta ta shirya a kashe mijinta ne domin ta koma gidan tsohon mijinta mai sun Idris Garba da suka rabu.

Bayan sun amince su yi haka sai ita kanta Auta da mahaifin tsohon mijinta Garba Hassan da kanen garban, Garba Sahabi suka shirya yadda zasu kashe Shaho domin ta iya komawa gidan tsohon mijin nata.

Wayanda ake zargi sun bayyana wa yan sanda cewa lallai sune suka kashe Shaho. Sun bishi har cikin daji suka rika sararsa da adda da takobi sannan suna jibgarsa da gora da kokara har ya rasu.

Kwamishinan yansandar jihar yace a yanzu dai Auta, da Wayanda ake zargi na tsare a ofishin yan sanda sannan za a cigaba da Bincike daga bisani a kai su kotu don girbar abin da suka shuka.

Madogara Premium Times

Leave a Reply

%d bloggers like this: