Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta fara biyan ma’aikata albashi har da ƙarin da aka yi wa maaikatan kasar daga watan Mayu da mu ke ciki.



Ƙaramar ministan kwadago a Nkeiryka Onyejeocha ce ta bayyana haka yayu yayin da ta ke jawabi dangane da ranar ma’aikata da aka yi a yau.
Ta ce abin takaici ne yadda ya kasance sabon ƙarin albashin da aka yi bai fara aiki ba tun a baya, amma komai na shirin kankama kuma za’a fara biyan albashin da aka ƙara ba da jimawa ba.
A sau da dama ƙungiyoyin kwadago a Najeriya na ta kiraye-kiraye don ganin an yi ƙarin albashin ga ma’aikata.
Ƙungiyar na neman a mayar da mafi ƙarancin albashi ya koma naira 615,000.
Sai dai gwamnatin tarayya a jiya ta ce ta ƙara kashi 25, da kashi 35 ga rukuni shida ciki har da sojoji da ƴan sanda.
A gefe kuda kuwa gwamnan jihar Edo ya sanar da ƙara albashin zuwa naira 70,000.