Ƙungiyar dilallan man fetur a Najeriya IPMAN ta ce rikicin da ke faruwa a ƙasashen Iran da Isra’ila ne ya yi sanadin ƙarancin man fetur a Najeriya.



Sakataren kungiyar na ƙasa James Tor ne ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabiji na Arise dangane da ƙarancin man da ake fuskanta.
Ya ce rikicin da ke tsakanin kasashen biyu ne sila ta ƙarancin da tsadar man da ake fuskanta a kasar.
Kusan mako guda kenan da ake fuskantar ƙaranci da tsadar man fetur a Najeriya, wanda hakan ya tilastawa masu ababen hawa ƙara kudin sufuri.
Da yawa daga cikin ƴan kasar kuwa wasu sun ajiye ababen hawansu sakamakon karancin ma da ake fuskanta.
Sai dai a jiya gwamnatin tarayya ta ce zuwa yau Laraba za ta kawo karshen wahalar ma fetur da ake fuskanta.
Sai dai har kawo yau ɗin an ci gaba da fuskantar matsi da tsadar man duk da cewar gwamnatin ta sha alwashin kawo karshen matsalar